Za'a yin Sallar a cikin zaman dar-dar kasancewar ko a jiya Alhamis an yi dauki ba dadi tsakanin Palasdinawa da kuma jami'an tsaro yahudawan mamaya na Isra'ila, inda dariruwan mutane suka jikatta.
Palasdinawa dai sun daina sallah a harabar masallacin na Baitul Mukaddas domin kalubalantar matakan tsaron Isra'ila a masallacin.
A jiya ne dai Isra'ila ta kammala kwashe na'urorin gano karafan data kafa a masallacin.
Matakin janye na’urorin daga Masallacin na birnin Kudus na zuwa ne bayan da kasashen duniya suka bukaci kawo karshen rikicin, wanda su ka yi gargadin cewa, kan iya kaiwa har inda ba'a tsammani.